1 Thessalonians 4

1A karshe, ‘yan’uwa, muna karfafa ku kuma muna yi maku gargadi cikin Ubangiji Yesu. Yadda kuka karbi umarni a garemu game da yadda dole za kuyi tafiya kuma ku gamshi Allah, kuma a cikin wannan hanya ku tafi, ku kuma wuce haka. 2Domin kun san umarnin da muka baku cikin Ubangiji Yesu.

3Gama wannan ne nufin Allah: kebewar ku - cewa ku kauce wa zina da fasikanci, 4Cewa kowannenku ya san yadda zai rike mata tasa cikin tsarki da girmamawa. 5Kada kayi mata cikin zautuwar sha’awa ( kamar al’ummai wadanda basu san Allah ba). 6Kada wani ya kuskura yaci amanar dan’uwansa akan wannan al’amari. Gama Ubangiji mai ramuwa ne akan dukkan wadannan al’amura, Kamar yadda a baya muka yi maku kashedi kuma muka shaida.

7Gama Allah bai kira mu ga rashin tsarki ba, amma ga rayuwar tsarki. 8Domin haka, duk wanda yaki wannan ba mutane yaki ba, amma Allah, wanda ya bada Ruhunsa Mai Tsarki a gareku.

9Game da kaunar ‘yan’uwa, baku bukatar wani ya sake rubuta maku, gama ku da kanku Allah ya koyar da ku kaunar ‘yan’uwa. 10Ba shakka, kunayin haka ga dukkan ‘yan’uwa wadanda ke cikin dukkan Makidoniya. Amma muna gargadin ku ‘yan’uwa, kuyi haka bugu da kari. 11Kuma muna gargadin ku ‘yan’uwa kuyi kokari ku zauna a natse, ku kula da al’amuranku, kuyi aiki da hannuwanku, Yadda muka umarceku a baya. 12Kuyi haka domin tafiyar ku ta zama dai dai a gaban wadanda basu bada gaskiya ba, kuma ya zama baku cikin bukatar komai.

13Bamu so ku zama da rashin fahimta ba, ‘yan’uwa, game da wadanda sukayi barci, domin kada kuyi bacin rai kamar sauran wadanda basu da tabbacin abinda ke gaba. 14Domin idan mun bada gaskiya Yesu ya mutu kuma ya tashi, haka kuma tare da Yesu Allah zai maido da duk wadanda suka yi barci a cikinsa. 15Gama muna fada maku wannan daga maganar Ubangiji, cewa mu da muke a raye, da aka bari har zuwan Ubangiji, babu shakka ba za mu riga wadanda suka yi barci ba.

16Gama Ubangiji da kan sa zai sauko daga sama. Zai zo da muryar babban mala’ika, da karar kahon Allah, sai matattu cikin Almasihu su fara tashi. 17Sai mu da muke a raye, wadanda aka bari, tare dasu za’a fyauce mu zuwa cikin gizagizai, mu hadu da Ubangiji cikin sararin sama. Haka zamu cigaba da kasancewa da Ubangiji. Domin haka ku ta’azantar da juna da wadannan maganganu.

18

Copyright information for HauULB